Masar Ta Gindaya Sharadi Kafin Ta Inganta Alakarta Da Turkiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26659-masar_ta_gindaya_sharadi_kafin_ta_inganta_alakarta_da_turkiya
Ma'aikatar harakokin wajen Masar ta ce sharadin inganta alaka da Turkiya shi ne hukumomin Ankara su daina yin katsa landan a al'amuran cikin gidan Masar.
(last modified 2018-08-22T07:01:11+00:00 )
Dec 24, 2017 08:35 UTC
  • Masar Ta Gindaya Sharadi Kafin Ta Inganta Alakarta Da Turkiya

Ma'aikatar harakokin wajen Masar ta ce sharadin inganta alaka da Turkiya shi ne hukumomin Ankara su daina yin katsa landan a al'amuran cikin gidan Masar.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto Sameh Shoukry ministan harkokin wajen Masar na cewa babu wani canji da aka samu a alakar diplomasiya tsakanin kasashen Masar da Turkiya duk kuwa da cewa Alkahira nada ra'ayin lokaci ya yi da za a rage sabanin dake akwai tsakanin kasashen biyu.

Sameh Shoukry ya kara da cewa wajibi ne kasar Turkiya ta kawo karshen katsa landan din da take yi a al'amuran cikin gidan Masar kafin a dawo da alakar dake tsakanin kasashen biyu kamar yadda take a baya.

Alaka ta yi tsami ne tsakanin kasashen Turkiya da Masar tun bayan juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Mursi a shekarar 2013, bayan da hukumomin Turkiya suka yi kakkausar suka a kan  juyin mulkin.