Urdugan: Takunkumin Amurka Akan Sudan Zalunci Ne
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26715-urdugan_takunkumin_amurka_akan_sudan_zalunci_ne
Shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan wanda yake ziyara a kasar Sudan ya bayyana cewa Manyan Kasashen Duniya Suna Son Kafa Iko A Kasashen Musulmi
(last modified 2018-08-22T11:31:12+00:00 )
Dec 26, 2017 07:40 UTC
  • Urdugan: Takunkumin Amurka Akan Sudan Zalunci Ne

Shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan wanda yake ziyara a kasar Sudan ya bayyana cewa Manyan Kasashen Duniya Suna Son Kafa Iko A Kasashen Musulmi

Shugaban na kasar Turkiya ya kara da cewa makirce-makircen da kasashen duniya masu ji da karfi suke kitsawa, manufarta karkatsa kasashen musulmi domin shimfida iko a cikinsu.

Har ila yau, shugaba Rajab Tayyib Urdugan ya soki Amurka saboda takunkumin da ta kakabawa Sudan, tare da cewa; hakan ya jefa mutanen Sudan da dama cikin matsala.

Urdugan ya kara da cewa; Babu shakka takunkumin Amurka akan Sudan, zalunci ne, kuma ko badadade ko bajima azzalumai za su dandana sakamakon zaluncinsu.