Nijar : Ana Zaben Shugaban Kasa A Zagaye Na Biyu
-
'Yan takara Hama Amadu da Mahamadu Issufu
A jamhuriya Nijar, bayan wata guda da gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na farko, yau ne al'ummar kasar da suka tantanci kada kuri'a ke zaben shugaban kasa a zagaye na biyu.
Za'a dai je zagaye na biyu na zaben ne bayan da aka kasa samun dan takara daya samu kuri'un da ake bukata don lashe zaben tun zagayen farko.
Zaben dai na yau shi ne irin sa na farko da aka tunkara a cikin rudani kasancewar kawancen jam'iyyun adawa na COPA sunyi kira ga magoya bayan su ga kauracewa zaben, saboda magudin da aka yi a zagayen farko da kuma ci gaba da tsare dan takara su Hama Amadou.
Hama Amadu dai na jinya a wani asibiti Faransa, bayan tabarbarewar yanayin lafiyar sa a gidan kurkukun Filangue inda aka tsare shi sama da watanni hudu bisa zargin cinikin jarirai.
A cikin irin wannan yanayin fitowar al'umma a zaben ne kawai zai fayace armashin sa, yayin da kawancen jam'iyyu masu mulki da shugaba Muhamadou Issoufou ke jagoran ke watsi da zarge-zargen na 'yan adawa.