Masar: Kungiyar Da'esh Ta Dauki Nauyin Kai Wa Majami'ar Kibdawa Hari
Dec 30, 2017 06:52 UTC
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto shafin "A'amak" mai kusanci da Da'esh yana sanar da dauke nauyin kai wa majami'ar Mar-mina hari
A jiya juma'a ne dai 'yan ta'addar suka kai wa majami'ar da take a yankin "Helwan" a kudancin alkahira, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 10 da kuma jikkatar wasu da dama.
Yan sandan kasar ta Masar sun sanar da kashe daya daga cikin maharan, yayin da su ke bin sawun na biyu.
Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa Ahmad Abulgaidh ya fitar da bayani da a ciki ya yi Allah wadai da harin ta'addancin.
A ranar 4 ga watan Nuwamba ma an kai wani mummunan harin ta'addanci a masallacin Sufaye wanda ya ci rayukan mutane 305 da jikkata wasu 128.
Tags