Kasashen Habasha Da Qatar Sun Tattauna Kan Karfafa Matakan Tsaro A Tsakaninsu
(last modified Sat, 30 Dec 2017 12:13:48 GMT )
Dec 30, 2017 12:13 UTC
  • Kasashen Habasha Da Qatar Sun Tattauna Kan Karfafa Matakan Tsaro A Tsakaninsu

Kasashen Habasha da Qatar sun tattauna kan hanyoyin karfafa matakan tsaro da na soji a tsakaninsu.

A ganawar da ta gudana tsakanin shugaban kasar Habasha Haile Mariam Dessalegn da shugaban rundunar sojin kasar Qatar Ghanim bin Shaheen Al-Ghanim a birnin Adis Ababa fadar mulkin kasar Habasha; Bangarorin biyun sun tattauna hanyoyin karfafa alaka a tsakanin kasashensu musamman a fuskar tsaro da karfin soji, inda suka cimma matsaya kan batutuwan biyu.

Har ila yau bangarorin kasashen biyu sun cimma wasu tarin yarjejeniya a tsakaninsu da nufin bunkasa ci gaban kasashensu.