Mahukuntan Masar Sun Rataye Wasu Fursunoni Hudu Saboda Ayyukan Ta'addanci
Jami'an tsaron kasar Masar sun sanar da cewa an zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutane hudu da wata kotu a kasar ta yanke wa hukumcin kisa saboda samunsu da laifi sanya bama-bamai a kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewar a yau Talata ce aka zartar da hukuncin kisa a kan wadannan mutane hudu wadanda a baya wata kotun soji ta yanke wa hukuncin kisa saboda samunsu da hannu cikin sanya bama-bamai a wani filin wasa a shekara ta 2015 a arewacin birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar din.
A yayin wannan aikin ta'addancin dai ta ya faru a filin wasan, wasu sojoji da suke karatu a kwalejin soji na Alkahira sun rasa rayukansu.
Zartar da hukuncin kisan na yau dai ya zo 'yan kwanaki bayan da aka zartar da hukuncin kisa a kan wasu 'yan ta'addan su 15.
Daruruwan jami'an tsaron Masar din ne dai aka kashe tun bayan da aka kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muhammad Morsi sakamakon hare-haren ta'addanci da ake kai musu.