Gwamnatin Kasar Habasha (Ethiopia) Za Ta Sako Fursunoni Na Siyasa na Kasar
Gwamnatin kasar Habasha (Ethiopia) ta sanar da cewa za ta yi watsi da dukkanin tuhumar da ake yi wa fursunoni na siyasa na kasar da kuma sako su bugu da kari kan rufe gidan yarin ihunka banza na kasar a shirin da take da shi na share fagen fadada fagen siyasa da demokradiyya a kasar.
Firayi ministan kasar Habashan Hailemariam Desalegn ne ya sanar da hakan bayan kwanaki na tattaunawa tsakanin 'ya'yan jam'iyyar Ethiopian People’s Revolutionary Democratic Front (EPRDF) mai mulki.
Firayi ministan wanda ya sanar da hakan a wata ganawa da yayi da manema labarai a jiya Laraba inda yace za a sako fursunonin siyasa da ake tsare da su da kuma yin musu shari'a kamar yadda kuma ya ce za a rufe gidan yarin nan na ihunka banza na Mae’kelawi wanda ya ce za a mai da shi gidan tarihi.
Har ila yau firayi ministan ya ce sauran fursunoni na siyasa da aka riga aka yanke musu hukunci ma za a yi musu afuwa don share fagen tattaunawa ta kasa da samar da yanayi mai kyau don gudanar da tsarin demokradiyya a kasar.
An jima dai ana zargin gwamnatin Ethiopian da take hakkokin 'yan adawa da kuma ci gaba da tsare su.