An Hallaka 'Yan Ta'adda A Gabashin Lardin Al-Arish Na Masar
Majiyar Tsaron Kasar Masar ta sanar da hallaka wani adadi na 'yan ta'adda a wani sumame da sojojin kasar suka kai a lardin gashin Al-Arish dake jihar Sinai ta arewa.
Kafar watsa labaran Alyaumu-Sabi'i ta nakalto majiyar tsaron kasar Masar a wannan Litinin na cewa dakarun tsaron kasar sun kai wani sumame a yankin Shalihati-sa'ad na gabashin Al-arish, biyo bayan sahun wasu gungun 'yan ta'adda da suka yi, inda suka hallaka takwas daga cikin su.
Bayan wannan bayyani wannan sanarwa babu wani cikekken bayyani da majiyar tsaron ta yi .
Jahar Sinai ta arewa ta zamanto wata maboyar kungiyoyin 'yan ta'adda musaman ma masu alakar da kungiyar ta'addancin nan ta ISIS a kasar Masar, lamarin da ya sanya jami'an tsaron kasar ta Masar suka karfafa kai hare-hare a can.
Kimanin shekaru uku kenan da jahar Sinai ta arewan ta kasance wani fagen yaki tsakanin kungiyoyin 'yan ta'adda da jami'an tsaron kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dariruwan jami'an 'yan sanda da sojojin kasar ta Masar.