Masar Tayi Hasarar Milyoyin Daloli Sanadiyar Rashin Tsaro
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27409-masar_tayi_hasarar_milyoyin_daloli_sanadiyar_rashin_tsaro
Shugaban Kasar Masar ya sanar da cewa kasarsa tayi hasarar milyoyin daloli cikin tsahon shekaru bakwai na rashin tsaro da rikicin siyasa da kasar ke fama da su.
(last modified 2018-08-22T07:01:18+00:00 )
Jan 19, 2018 08:14 UTC
  • Masar Tayi Hasarar Milyoyin Daloli Sanadiyar Rashin Tsaro

Shugaban Kasar Masar ya sanar da cewa kasarsa tayi hasarar milyoyin daloli cikin tsahon shekaru bakwai na rashin tsaro da rikicin siyasa da kasar ke fama da su.

Cikin wani jawabi da ya  gabatarwa 'yan kasar a jiya alhamis, Shugaba Abdulfatah Alsise na kasar Masar ya bayyana cewa cikin shekaru 7 da suka gabata, kasar ta yi hasarar miliyan 80 zuwa 90 na dalar Amurka sanadiyar matsalar tsaro da kuma rikicin siyasa da kasar ke fama da su.

Yawan buda ido da kasar ta dogara da shi wajen samun kudaden shiga da kuma samarwa da milyoyin matasan kasar aikin yi ya fuskanci koma baya saboda matsalar tsaro da kasar ke fama da shi.

Daga shekarar 2011 zuwa yanzu kasar ta yi hasara mai dunbun yawa sakamakon rikicin siyasa da matsalar tsaro kamar yadda Shugaba Alsise ya bayyana, sannan kuma ya dauki kudirin ci gaba da yaki da ta'addanci har sai tsaro da konciyar hankali ya dawo a kasar ta Masar.