Matan Togo Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati
(last modified Sun, 21 Jan 2018 19:10:24 GMT )
Jan 21, 2018 19:10 UTC
  • Matan Togo Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati

Bisa bukatar gamayyar jam'iyun 'yan adawa, duban matan kasar Togo ne suka gudanar da zanga-zangar kin jinin Gwamnati jiya Asabar a birnin Lome fadar milkin kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga birnin Lome na kasar Togo ya habarta cewa dubun dubutan matan kasar ne suka fito zanga-zanga a jiya asabar domin nuna adawar su da yanayin da kasar ta shiga a yau, tare kuma da neman shugaba Faure Gnassingbé ya yi murabus daga kan mikaminsa.

Har ila yau, mahalarta zanga-zangar sun bukaci gwamnati ta gaggauta samar da canji a kasar ko kuma tayi murabus.

Rahotanni sun ce jam'iyun siyasa 14 suka shirya wannan zanga-zanga, da ko wani mako suke gudanar da irinta domin  neman canji a kasar, saidai har yanzu babu wani martani da ya fito daga ofishin shugaban kasar ta Togo.

Sama da watani hudu kenan da 'yan kasar ta Togo suke gudanar da zanga-zangar neman canji tare da kawo karshen milkin shekaru 50 na gidan Gnassingbé.