Sudan Ta Musunta Zargin Amurka Kan kare Hakkin bil Adama
Kasar Sudan ta musunta zargin da Amurka ta yi mata dangane da kare hakkokin bil Adama.
Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta nuna rashin jin dadi, game da sukar da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi inda take cewa Amurkar ta gaza fahimtar irin ci gaba da aka samu a fannonin kare martabar bil Adama, da ikon furta albarkacin baki a kasar.
Sudan ta ce yanzu haka akwai jaridu kusan 20 da ke fita duk ranar Allah a kasar, wadanda ke kunshe da ra'ayoyin siyasa mabanbanta, masu dauke da ra'ayoyin 'yan kasar na kashin kan su.
A ranar Juma'a ne dai ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta yi Allah wadai da tsare wasu 'yan jarida a kasar ta Sudan, bayan da aka zarge su da dauko labarai game da zanga zangar da ta biyo bayan hauhawar farashin kayan masarufi.