Gudanar Da Sauyi A Rundunar Tsaron Kasar Nijar
Shugaban kasar Nijar ya gudanar da gagarumin sauyi a bangaren tsaron kasar da nufin yaki da ta'addanci.
A farkon shekarar nan, a yayin jawabinsa na murnar sabuwar shekara, Shugaba Issoufou Mahamadou na jamhoriyar Nijar ya yi wa al'ummar kasar alkawarin karfafa dakarun tsaron kasar domin kalubalantar barazanar tsaro da kuma ci gaba da yaki da ta'ddanci a kasar,
A makon farko, na wannan wata da muke ciki, shugaba Issoufou Mahamadou ya nada Janar Ahmad Muhamad a matsayin babban hafsan sojojin kasar bayan da tsohon babban hafsan sojojin kasar ya yi ritaya, sannan kuma ya nada janar Ibrah Boulama Issa a matsayin mataimakin babban hafsan sojojin kasar ta Nijar kuma babban hafsan sojojin kasa na kasar, har ila yau shugaba Issoufou ya sauya babban kwamandan rundunar tsaron Jandarma ta kasar, a ranar juma'a 12 ga wannan wata na Janairu, shugaban kasar ya nada birgediya janar Iro Oumaru a matsayin babban komandan dakarun tsaron fadar shugaban kasa.
Wannan sauye-sauye na zuwa ne a yayin da kasar ke fuskantar barazanar tsaro daga kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da kuma masu da'awar jihadi na kasar Mali a iyakokin yammacin kasar, da kuma mayakan kungiyar boko haram a iyakokin kudu maso gabashin kasar, sai kuma matsalar masu safarar mutane zuwa kasashen Turai da masu safarar makamai da miyagun kwayoyi a yankin sahara na arewacin kasar.
A cikin shekaru biyu da suka gabata, kasar ta Nijer ta fuskanci hare-haren ta'addanci daga kungiyoyin 'yan ta'adda na kasar Mali da kuma Boko haram a yankin tabkin Chadi, inda ko a makon da ya gabata mayakan boko haram din suka kaddamar da wani mumunan hari kan sojojin na Nijar a garin Toummour na jihar Diffa tare da kashe sojoji akalla bakwai da kuma jikkata wasu da dama na daban.
Duk da irin kokarin da gwamnati ke yi na magance matsalar tsaro a kasar da ma yankin baki daya, ta hanya bayar da dama ga kasashen Turai da Amurka suka kafa sansanin sojojinsu a kasar, hakan ya fuskanci suka daga masana tsaro na ciki da wajen kasar, inda masanan ke ganin cewa bai kamata ba hukumomin kasar ta Nijar su mayar da kasar wata kasuwar baje koli na dakarun tsaron kasashen waje, a maimakon hakan kamata ya yi gwamnatin ta Nijar ta samar wa dakarun kasar makaman zamani tare da basu horo kan yadda za su tunkari 'yan ta'addar.
A bangare guda kuma, kasar ta Nijar na daga cikin kasashe biyar da suka kafa rundunar yaki da ta'addanci a yankin sahel bisa jagorancin kasar Faransa, a halin da ake ciki dai, al'ummar kasar ta Nijar na kyautata fatan cewa wannan sauyi zai zamewa kasar alheri a bangen tsaro da kuma yaki da ta'addanci.