Babban Dan Takarar Shugabancin Masar Ya Janye Takararsa Bisa Zargin Musgunawa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27635-babban_dan_takarar_shugabancin_masar_ya_janye_takararsa_bisa_zargin_musgunawa
Babban dan takarar da ake ganin zai kalubalanci shugabancin kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi a zaben shugaban kasar da za a gudanar, wato Khaled Ali, ya sanar da janyewarsa daga takarar shugabancin kasar yana mai zargin cin zarafin magoya bayansa da kuma rashin tabbacin gudanar da ingantaccen zabe a kasar a matsayin dalilansa na janyewar.
(last modified 2018-08-22T07:01:20+00:00 )
Jan 25, 2018 14:12 UTC
  • Babban Dan Takarar Shugabancin Masar Ya Janye Takararsa Bisa Zargin Musgunawa

Babban dan takarar da ake ganin zai kalubalanci shugabancin kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi a zaben shugaban kasar da za a gudanar, wato Khaled Ali, ya sanar da janyewarsa daga takarar shugabancin kasar yana mai zargin cin zarafin magoya bayansa da kuma rashin tabbacin gudanar da ingantaccen zabe a kasar a matsayin dalilansa na janyewar.

 Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar Khaled Ali, wanda kuma lauya ne ya sanar da janyewar tasa ne cikin wata sanarwa da yayi a birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar din  inda ya zargin hukumar zaben kasar da goyon bayan shugaba Sisi; kamar yadda kuma ya ce ana ci gaba da musguna wa magoya bayansa duk da nufin tsoratar da su.

Sanarwar Khaled Ali din ta zo ne bayan da shugaba Sisin ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar Masar din a zaben da za a gudanar a watan Maris mai kamawa.

Janyewar Khaled Ali daga takarar shugabancin kasar Masar din da kuma kama tsohon babban hafsan sojojin kasar da ya sanar da aniyarsa ta takarar a shekaran jiya, hakan ya sanya a halin yanzu dai shugaba Sisi din wanda aka zaba a shekara ta 2014 a matsayin sabon shugaban kasar Masar din bayan juyin mulkin da yayi wa hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi, zai zamanto shi ne kawai dan takara guda daya tilo a zaben shugaban kasar da na wata Maris din.