An Zabi Shugaban Rwanda A Matsayin Sabon Shugaban Tarayyar Afirka
An zabi shugaban kasar Rwanda Paul Kagame a matsayin sabon shugaban kama-kama na kungiyar Tarayyar Afirka (AU) wanda zai maye gurbin shugaba Alpha Conde na kasar Guinea Conakry inda yayi alkawarin samar da sauye sauye a tsarin gudanar da Afirka ciki kuwa har da batun 'yancin zirga-zirga tsakanin 'yan Afirkan.
A jiya Lahadi ne dai aka zabi shugaba Kagamen a matsayin sabon shugaban kungiyar ta AU na shekara guda a taron da shugabannin Afirkan suka gudanar a birnin Addis Ababa, helkwatar kungiyar ta AU inda a jawabin da ya yi na karbar shugabancin AU din yayi alkawarin samar da sauyi da kuma share fagen 'yancin zirga-zirga tsakanin 'yan kasashen Afirkan.
Har ila yau kuma sabon shugaban kungiyar ta AU ya ce daga cikin tsare tsaren da yake da shi har da share fagen ba wa matasan Afirkan da suke da kwarewa a fannoni daban-daban damar ba da ta su gudummar wajen ciyar da nahiyar gaba, kamar yadda kuma yayi alkawari tabbatar da hakkokin mata da kuma ba su fagen ba da ta su gudummawar.
A bisa tsari dai ana zaban shugaban kungiyar ta AU ne dai a taron shugabannin Afirkan wanda kuma zai rike shugabancin na tsawon shekara guda ne kafin a sake yin wani zaben da ba wa wani shugaban na daban wannan matsayi.