Nijer:Harin Boko Haram Ya Hallaka Mutane 3 A Garin Chétimari
Cikin wata sanarwa da majiyar tsaron Nijar ta fitar a jiya talata jami'an tsaro biyu ne da wani yaro suka rasa rayukansu sanadiyar harin da kungiyar boko haram suka kai kan babura 10 akan sansanin soja da ke garin Chétimari na jahar Diffa dake kudu maso gabashin kasar.
Sanarwar ta ce a marecen ranar Litinin din da ta gabata ce mayakan boko haram kan babura 10 suka kai hari akan sansanin soja na garin Chétimari mai nisan kilomita 25 da garin Diffa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar sojoji biyu da wani yaro guda bayan da harshashi ya fada gidansu, bayan turjiya da suka fuskanta daga jami'an tsaro, mayakan na boko haram sun janye, amma sun yi awan gaba da wasu motocin soja.
A tsakiyar watan nan na Janairu ma dai, maharan na Boko haram sun kai hari a yankin Toummour da ke gabacin Diffa a gabar tafkin Chadi tare da kashe sojojin kasar 7 da jikkata wasu 17.
Yankin Diffa yana daga cikin yankunan da kungiyar ta Boko haram take yawan kai wa hare-hare a cikin Jamhuriyar Nijar.