Aljeriya: An Kashe Daya Daga Cikin Kwamandojin Al'ka'ida
Feb 01, 2018 06:55 UTC
Ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ce ta sanar da kashe wani kusa mai kula da harkokin wa'azi da watsa labarai na kungiyar al'ka'ida a arewacin Afirka.
Ma'aikatar tsaron ta Aljeriya ta ci gaba da cewa; An kashe Abu Hisham Abu Rawaha ne a wani wuri da yake da nisan kilo mita 400 daga babban birnin kasar Ajes.
Tun a 1994 ne jami'an tsaron kasar ta Aljeriya suke neman Abu Hisham ruwa a jallo saboda ayyukansa na ta'addanci.
Sojojin Aljeriyan sun kuma sanar da kashe wani 'yan ta'addar biyu a yankin Madiyyah a kudancin kasar.
A yankin Khanshalah ma sojojin Aljeriya sun kashe wasu 'yan ta'adda 8 masu hatsari.
Tags