Nijar : Mahamadu Isufu Ya Lashe Zabe Da Kashi 92.49%
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2788-nijar_mahamadu_isufu_ya_lashe_zabe_da_kashi_92.49
Hukumar zabe mai zamen kan ta a jamhuriya Nijar (CENI) ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka kada kuria'a a Ranar lahadi data gabata inda shugaban kasar mai barin gado Mahamadu Isufu na Jamiyyar PNDS tarayya ya lashe zaben da kashi 92.49%
(last modified 2018-08-22T06:58:01+00:00 )
Mar 22, 2016 12:38 UTC
  • Shugaba Mahamadu Isufu da shugaban hukumar zabe CENI Bube Ibrahim
    Shugaba Mahamadu Isufu da shugaban hukumar zabe CENI Bube Ibrahim

Hukumar zabe mai zamen kan ta a jamhuriya Nijar (CENI) ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka kada kuria'a a Ranar lahadi data gabata inda shugaban kasar mai barin gado Mahamadu Isufu na Jamiyyar PNDS tarayya ya lashe zaben da kashi 92.49%

Babban abokin hamayyar sa Hama Amadu dake jinya a Faransa bayan tabarbarewar kiwan lafiyar sa a gidan kurkukun da yake tsare kafin a fitar da shi waje ya samu kashi 7,5% na sakamakon kuri'un da aka kada.

Sakamakon ya kuma nuna cewa kashi 59.7 an al'umma ne suka fito zaben da 'yan adawa suka kauracewa saboda magudin da aka yi a cewar su a zagayen farko da kuma ci gaba da tsare dan takara su Hama Amadou.

bayanai da dama daga wannan kasa sun nuna cewa kiran da ‘yan adawa suka yi wa magoya bayansu na su kauracewa zaben ya yi tasiri domin an samu karancin fitowar masu kada kuri’a sosai a zaben musamman a mayan biranen kasar ciki harda Yamai babban birnin kasar.

Babban kalubalen daka a gaban zababen shugaban kasar a yanzu shi ne hada kan al'ummar kasar daya rabu sakamakon cacar bakin da akayi tayi gabanin zaben da matsalar tsaro sai uwa uba talaucin daya dabaibaiye tafiyar kasar.