Sojojin Masar Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 16 A Tsbirin Sinai
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28121-sojojin_masar_sun_hallaka_'yan_ta'adda_16_a_tsbirin_sinai
Dakarun tsaron kasar Masar sun sanar da hallaka 'yan ta'adda 16 a wani sumame da suka kai yankin tsibirin Sinai.
(last modified 2018-08-22T07:01:24+00:00 )
Feb 11, 2018 08:24 UTC
  • Sojojin Masar Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 16 A Tsbirin Sinai

Dakarun tsaron kasar Masar sun sanar da hallaka 'yan ta'adda 16 a wani sumame da suka kai yankin tsibirin Sinai.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto rundunar tsaron Masar a wannan Lahadi na cewa bisa umarnin shugaban kasar Abdel Fattah el-Sisi sun kai wani sumame na musaman yankin tsibirin Sinai, inda suka hallaka 'yan ta'adda 16 tare da kame wasu 30 da ake zarkin 'yan ta'adda ne a yankin.

Har ila yau sanarwar dakarun tsaron Masar din ta bukaci hadin kan al'ummar kasar domin kawo karshen 'yan ta'adda a yankin na Sinai, sannan kuma sun bukaci ilahirin jami'an 'yan sanda da sojojin kasar da su kasance cikin shirin ko ta kwana domin a ko da yaushe ana iya kiransu domin kalubalantar 'yan ta'adda.

Tun bayan da juyin milkin da shugaba Abdel Fattah el-Sisi ya yi a shekarar 2013, kasar ta Masar ta fara cikin rikci.