Shugaba Nguesso Na Kan Gaba A Zaben Shugaban Kasar Kongo
(last modified Wed, 23 Mar 2016 10:08:18 GMT )
Mar 23, 2016 10:08 UTC
  • Shugaba Nguesso Na Kan Gaba A Zaben Shugaban Kasar Kongo

Rahotanni daga kasar Kongo na nuni da cewa shugaban kasar Denis Sassou Nguesso shi ne kan gaba da gaggarumin rinjaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Lahadi da ta gabata, duk kuwa da zargin da 'yan adawa suke yi na tafka magudi.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar shugaban hukumar zaben kasar Henri Bouka ya bayyanawa manema labarai cewa sakamakon da aka samu daga gundumomi 72 cikin 111 na kasar na nuni da cewa cewar Denis Sassou Nguesso, wanda ya mulki kasar Kongon na tsawon shekaru 32 ya sami kashi 67 cikin dari na kuri'un da aka kada.

Tsohon minista Guy Brice Parfait Kolelas shi ne ya zo na biyu da kashi 16.8. A na sa ran yau zuwa gobe ne dai za a gama kidayen sauran kuri'un inda shugaba Nguesson yake bukatar ya sami gaggarumin rinjaye a kan abokan takararsa takwas muddin baya son a kai ga zagaye na biyu.

Madugun gamayar 'yan adawan kasar Charles Bowao yayi watsi da sakamakon zaben yana mai cewa a wani lokaci a yau din nan Laraba za su fitar da nasu sakamakon zaben abin da gwamnatin ta ce ya saba wa doka.