Masar: Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'adda 15 A Yankin Sina
Feb 14, 2018 15:29 UTC
Majiyar sojan Masar ta sanar da kashe 'yan ta'addar a wani hari da ta kai a yau laraba a yankin Sina. Majiyar ta ci gaba da cewa an lalata mabuyar 'yan ta'adda har guda 11.
Bugu da kari jami'an tsaron kasar ta Masar sun sanar da kame 'yan ta'adda 150. Haka nan kuma sun kama sanadarin C4 mai fashewa har kilo 500.
A ranar juma'ar da ta gabata ne dai sojojin Masar suka bude gagarumin farmaki akan sansanonin 'yan ta'adda a jahohi uku na kasar. Yankin Sina mai iyaka da Palasdinu yana a matsayin sansanin 'yan ta'adda masu alaka da kungiyoyin al'ka'ida da kuma Isis.
A lokutan daban-daban suna kai wa sojojin kasar hari a yankuna daban-daban da suka hada da Alkahira.
Tags