Firayi Ministan Kasar Habasha Ya Yi Murabus Daga Kan Mukaminsa
Firayi ministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn ya yi murabus daga kan mukaminsa a yau Alhamis, kamar yadda babbar tashar talabijin din gwamnatin kasar ta sanar.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, baya ga sauka daga kan shugabancin gwamnatin Habasha, Hailemariam Desalegn kuma ya sauka daga shugabancin kawancen jam'iyyun siyasa da suka kafa gwamnati.
Har yanzu babu wani bayani a hukumance dangane da dalilan da suka sanya Firayi ministan na kasar Habasha yin murabus, amma dai anan ganin hakan ba zai rasa nasaba da boren da ake ta yi a manyan yankunan kasar ba, inda miliyoyin jama'a ke nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin nasa, musamman ma yadda suke ganin ya gaza wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, da kuma batun cin hanci da ya addabi wasu bangarori na gwamnati a kasar.
Kamar yadda kuma Hailemariam Desalegn ya rasa goyon bayan wasu daga muhimman 'yan siyasa da suka mara masa baya kuma suka hada kawance da shi har kai ga wannan matsayi.