Congo Braza : An Kori Manyan Alkalan Kasa Bakwai
(last modified Wed, 21 Feb 2018 05:55:18 GMT )
Feb 21, 2018 05:55 UTC
  • Congo Braza : An Kori Manyan Alkalan Kasa Bakwai

Majalisar Koli ta alkalan kasa a Congo Brazaville, ta kori wasu manyan alkalan kasar bakwai daga bakin aiki, bisa tafka manyan kura-kurai.

An sanar da daukan wannan matakin ne a zaman majalisar da shugaban kasar Denis Sassou N'Guesso, ya jagoranta.

Ba'a dai bayyana sunayen al'kalan ba, amma a cewar ministan shari'a na kasar, Ange Aimé Wilfrid Bininga, dukkansu bakwai an sallame su saboda tabka manyan kura-kurai akan aikinsu.

A cikin batutuwa kama da hakan da kwamitin da'a na majalisar alkalanci ta kasar ya gabatar, an kuma ragewa wasu manyan alkalai biyu matsayi, kana kuma an canzawa wasu uku wurin aiki saboda karbar kudi don sallamar wasu fursuna.

Bayanai sun ce 'yan kasar da dama dai sun yi maraba da wannan matakin da ke da manufar tsara aikin alkalai a kasar dake fama da matsalar rashawa.