Congo : N'Guesso Ya Lashe Zabe Tun Zagayen Farko
Shugaban kasar Congo Denis Sassou Nguesso ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi ranar lahadi a kasar da kashi 60% na kuri'un da aka kada.
Wannan sakamakon dai ya baiwa shugaban kasar mai barin gado daya shafe shekarau 32 kan madafun iko lashe zaben tun a zagayen farko kamar yadda ministan cikin gida na kasar Raymond Zéphyrin Mboulou ya sanar a cikin daren jiya.
Sakamakon da aka sanar ya kuma nuna cewa Guy-Brice a mastayin wanda ya zo matsayi na biyu a zaben da kashi sama da 15%, yayin da Janar
Jean-Marie Michel Mokoko ya zo na uku a zaben da kashi kashi 14%.
Dama kafin hakan 'yan takara biyu sunyi fatali da kwarya-kwarya sakamakon da hukumar zaben kasar ta sanar, inda suke bukatar da a sake kidayar kuri'un.
Mr Nguessou mai shekaru 72 a duniya ya sake tsayawa takara ne a zaben shugaban wannan kasar ta Congo ne bayan gyaren fuska da akayi wa kundin tsarin mulkin kasar da 'yan adawa ke yi wa kyallon wani juyin mulki.