Sabon Rahoton MDD Akan Take Hakkin Bil'adama A Kasar Sudan Ta kudu
(last modified Sat, 24 Feb 2018 06:46:41 GMT )
Feb 24, 2018 06:46 UTC
  • Sabon Rahoton MDD Akan Take Hakkin Bil'adama A Kasar Sudan Ta kudu

A jiya juma'a ne Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar da rahoto da a ciki ta bayyana cewa yadda ake ci gaba da take hakkin bil'adama a kasar Sudan ta kudu

Rahoton ya bijiro da dalilai daga bangaren gwamnati da kuma na 'yan tawayen dangane da take hakkin bil'adama, tare da zargin shugaban kasa da jami'an soja 40 da kuma gwamnoni uku a matsayin wadanda su ke da hannu a ciki.

Daga cikin laifukan da ake zargin mutanen da aikatawa da akwai cin zarafi da yin fyade, da kuma musgunawa mutane ta hanyar amfani da karfi.

Shekaru biyar kenan a jere ana yakin basasa a tsakanin sojoji masu biyayya ga shugaban kasa Silva kiir da tsohon mataimakinsa Reikh Machar.