Nijar : Mahamadu Isufu Ya Yi Kira Kan Kafa Gwamnatin Hadin Kai
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2857-nijar_mahamadu_isufu_ya_yi_kira_kan_kafa_gwamnatin_hadin_kai
Shugaban jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou ya ce a shirye ya ke domin kafa gwamnatin hadin-kan kasa da za ta kunshi 'yan adawa domin tunkarar kalubalolin dake gaban wannan kasa.
(last modified 2018-08-22T06:58:01+00:00 )
Mar 24, 2016 01:24 UTC
  • shugaba Mahamadu Isufu na Nijar
    shugaba Mahamadu Isufu na Nijar

Shugaban jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou ya ce a shirye ya ke domin kafa gwamnatin hadin-kan kasa da za ta kunshi 'yan adawa domin tunkarar kalubalolin dake gaban wannan kasa.

Shugaban wanda ke bayyana hakan bayan nasarar da ya yi a zaben da aka gudanar zagaye na biyu a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce aiki tukuru domin shawo matsalolin da suka dabaibaiye kasar shi ne abun maida hankali akai don lokacin cacar baki ya wuce.

A tattaunawar da kanfanin dilancin labaren AFP shugaba Issufu ya zayano wasu matsalolin da a cewar sa ke zama karfen kafa a ga ci gaban kasar da suka hada da tsaro, ci gaban kasa da tattalin arziki.

To saidai ayar tambayar da dumbin al'umma kasar ke azawa ita ce, ko ta yaya shugaban kasar zai ciwo kan 'yan adawar kasar ta suka bayyana cewa daga ranar daya ga watan Afirilu, ranar da wa'adin shugaban kasar na farko zai cika, babu halastacen shugaban kasa da zasu yi wa biyaya, domin a cewarsu ba a gudanar da zabe yadda ya kamata ba.

A ranar Talata data gabata ne hukumar zaben kasar ta sanar da cewa shugaban Mahamadu Isufu ya lashe zaben shugaban kasar zagaye na biyu da kashi 92% yayin da babban abokin hamayar sa Hama Amadu ya samu kashi 7% na kuri'un da aka kada.