Shugaban Kasar Masar Ya Yi Kwaskwarima Wa Majalisar Ministocinsa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2863-shugaban_kasar_masar_ya_yi_kwaskwarima_wa_majalisar_ministocinsa
Rahotanni daga kasar Masar sun bayyana cewar shugaban kasar Abdel Fattah al-Sisi ya yi kwaskwarima wa majalisar Ministocinsa inda ya nada sabbin ministoci 10 ciki kuwa har da ministan kudi da zuba jari inda tuni sabbin ministocin suka yi rantsuwar kama aiki.
(last modified 2018-08-22T06:58:01+00:00 )
Mar 24, 2016 05:02 UTC
  • Shugaban Kasar Masar Ya Yi Kwaskwarima Wa Majalisar Ministocinsa

Rahotanni daga kasar Masar sun bayyana cewar shugaban kasar Abdel Fattah al-Sisi ya yi kwaskwarima wa majalisar Ministocinsa inda ya nada sabbin ministoci 10 ciki kuwa har da ministan kudi da zuba jari inda tuni sabbin ministocin suka yi rantsuwar kama aiki.

A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar wanda kuma gidan talabijin din kasar ya watsa ta bayyana cewar an nada kwararre a fannin aikin bankin nan Amr el-Garhy a matsayin ministan kudi , yayin da Dalia Khorshid kuma an bata mukamin ministar harkokin zuba jari.

Sauran mukaman da shugaba al-Sisi ya bayar sun hada da ministoci a ma'aikatun shari'a da na harkokin yawon bude ido da al'adu da harkokin aikin gwamnati da ayyukan noman rani da sufurin jiragen sama da na kasa.

Shugaba Al-Sisin ya dau wannan matakin ne dai a kokarinsa na sake farfado da tattalin arzikin kasar da kuma fada da rashawa da cin hanci da yake ci gaba da ta'annuti ga tattalin arzikin kasar.