Masar: Hatsarin Jirgin Kasa Ya Ci Rayuka 18
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28657-masar_hatsarin_jirgin_kasa_ya_ci_rayuka_18
Majiyar sufuri daga kasar Masar din ta ce jirage kasa biyu ne suka yi karo da juna a gundumar al-Buhairah inda nan take mutane 18 suka kwanta dama.
(last modified 2018-08-22T07:01:29+00:00 )
Feb 28, 2018 15:26 UTC
  • Masar: Hatsarin Jirgin Kasa Ya Ci Rayuka 18

Majiyar sufuri daga kasar Masar din ta ce jirage kasa biyu ne suka yi karo da juna a gundumar al-Buhairah inda nan take mutane 18 suka kwanta dama.

Rahoton ya kuma kara da cewa; Baya ga wadanda suka mutu an sami karin wasu mutanen 20 da suka jikkata.

Babban jami'in tafiyar da sha'anin mulki a gundumar ta al-Buhaira, Ala'u Abdulfattah ya ce; Hatsarin ya faru ne saboda ballewar da tarago biyu na jirgin mai cike da matafiya  su ka yi, kuma su ka ci karo da jirgin daukar kaya.

Hatsarin na yau ya faru ne dai kwanaki 20 gabanin gudanar da zaben shugaban kasa da ake tsammanin Abdulfattah al-sisy zai lashe.

Matsalolin tattalin arzikin da kasar ta Masar take fuskanta ya sa gwamnati ta yi watsi da yi wa jiragen kasa kwaskwarima bayan da suka tsufa.