Sojojin Masar Sun Halaka Yan Ta'adda 13 A Yankin Sinaa
Sojojin kasar Masar sun bada labarin halaka yan ta'adda kimani 13 a yankin Sinaa a yau Alhamis
Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto majiyar sojojin na masar tana bada wannan bayanin a yau Alhamis ta kuma kara da cewa sojojin kasar sun kai farmaki kan mabuyar yan ta'adda guda 9 a yankin Sina a yau Alhamis sun kuma kashe 13 daga cikinsu sannan sun kama wasu 86 da ransu.
Labarin ya kara da cewa rundunar ta rasa sojoji biyu a fafatawan da suka yi da yan ta'addan, sannan soja guda ya ji rauni. Tun ranar 9 ga watan Febreru da ya gabata ne sojojin kasar ta Masar suka fara wani shiri na musamman don share yan ta'adda a yankin na Sinaa.
Tun shekara ta 2013 ne yan ta'adda suka bulla a yankin Sinaa na kasar ta Masar ya zuwa yanzu kuma sun yi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaron kasar da dama, sun kuma kai hare-hare kan wurare masu yawa a yankin. Mafi muni daga cikinsu shi ne wanda ya halaka mutane kimani 300 a wani masallaci a garin Arish na yinkin.