'Yan Adawar Nijar Sun kaurace wa zaman sabuwar majalisar dokokin kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2881-'yan_adawar_nijar_sun_kaurace_wa_zaman_sabuwar_majalisar_dokokin_kasar
Daukacin 'yan majalisa da aka zaba karkashin jam'iyyun adawar a jumhoriyar Nijar sun kauracewa bikin girka sabuwar majalisar dokoki da ya gudana a birnin Yamai fadar milkin kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:01+00:00 )
Mar 24, 2016 12:24 UTC
  • 'Yan Adawar Nijar Sun kaurace wa zaman sabuwar majalisar dokokin kasar

Daukacin 'yan majalisa da aka zaba karkashin jam'iyyun adawar a jumhoriyar Nijar sun kauracewa bikin girka sabuwar majalisar dokoki da ya gudana a birnin Yamai fadar milkin kasar

'Yan Majalisun da aka zaba kalkashin inuwar jam'iyun adawa sun kaurace wa bikin girka sabuwar majalisar dokoki, kwanaki 33 bayan zaben 'yan majalisar da ya gudana a ranar 21 da kuma 22 ga watan Fabrairun 2016.cikin 'yan Majalisu 53 na bangaren adawa Babu ko da daya daga da ya halarci babban zauren taro na Palais des Congres na birnin Yamai inda bikin kafa sabuwar majalisar ya gudana.

yanzu haka dai a kwai Zababbun 'yan majalisa uku na bangaren adawa ne dake tsare a gidan kaso , bisa zarginsu da hanu a yunkurin juyin mulkin da aka yi kokarin yi a watan Disamba shekarar da ta gabata ba tare da cin nasara ba

Gamayyar jam'iyyun adawa ta COPA ta ki amincewa da sakamakon zabe zagayen farko da na biyu da suka gudana. Sai dai bangaren shugaba Mahamadou Issoufou da masu goyon bayansa na da cikakken rinjaye a wannan majalisa, inda kawancen da ke mulki ke da 'yan majalisa 118 daga 171 da majalisar ta kunsa.

A yau ne dai ake sa ran za a zabi sabon shugaban Majalisar dokokin kasar .