Masar: An Yanke Wa "Yan Adawa 10 Hukuncin Kisa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28965-masar_an_yanke_wa_yan_adawa_10_hukuncin_kisa
Jaridar "Yaun Sabi'i' da ake bugawa a Masar ta ce baya ga mutane 10 da aka yanke wa hukuncin kasar an kuma daure wasu biyar hukuncin daurin rai da rai.
(last modified 2018-08-22T07:01:32+00:00 )
Mar 10, 2018 15:34 UTC
  • Masar: An Yanke Wa

Jaridar "Yaun Sabi'i' da ake bugawa a Masar ta ce baya ga mutane 10 da aka yanke wa hukuncin kasar an kuma daure wasu biyar hukuncin daurin rai da rai.

Jaridar ta ci gaba da cewa; Mutanen da aka yanke wa hukuncin suna da alaka ne da rikice-rikicen da suka biyo bayan sauke Muhammadu Mursi daga kan mulki a 2014. An sami mutanen da laifin mallakar makamai da kafa kungiya domin kai wa cibiyoyin gwamnati hare-hare.

Wannan ba shi ne karon farko ba da aka yankewa 'yan hamayyar siyasa hukuncin kisa a kasar Masar, musamman wadanda suke da alaka da kungiyar Ikhwan Muslimin.

A shekarar 2013 ne dai sojojin kasar ta Masar karkashin Abdulfattah al-sisy su ka kifar da gwamnatin Muhammadu Mursi na kungiyar Ikhwanul Muslimin.