Nijar : Kungiyoyin Addinin Islama Sun Sa Baki A Takaddama Kan Dokar Haraji
Kungiyoyin addinin Islama a Jamhuriyar Nijar, sun yi kira ga bangarorin da ke ja in ja kan sabuwar dokar harajin kasar su zauna kan teburin sulhu don samar da zaman lafiya a kasar.
kungiyoyin sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da suka fitar a jiya Asabar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin aka samu rabuwar kai, tsakanin 'yan kasar kan sabuwar dokar ta haraji dake kunshe a kasafin kudin kasar na bana.
An dai shafe makwanni da dama ana zanga-zanga da jerin gwano a galibin manyan biraren kasar na nuna goyan bayan baya da kuma nuna kiyaya ga sabuwar dokar harajin.
Yau Lahadi ma dai hadin gwiwar wasu kungiyoyin fara hula a kasar dake samun goyan bayan jam'iyyun adawa sun kira gangami na nuna fishin kan dokar harajin, a yayin da a jiya aka gudanar da irin wannan gangami amma na nuna goyan bayan gwamnati a biranen Zinder da Maradi.