An Kashe 'Yan Ta'adda 16 A Tsibirin Sinai Na Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28979-an_kashe_'yan_ta'adda_16_a_tsibirin_sinai_na_masar
Rundunar tsaron Masar ta sanar da hallaka 'yan ta'adda 16 a wani farmaki da suka kai yankin tsibirin Sinai.
(last modified 2018-08-22T07:01:32+00:00 )
Mar 11, 2018 07:22 UTC
  • An Kashe 'Yan Ta'adda 16 A Tsibirin Sinai Na Masar

Rundunar tsaron Masar ta sanar da hallaka 'yan ta'adda 16 a wani farmaki da suka kai yankin tsibirin Sinai.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan lahadi, Rundunar tsaron kasar Masar ta sanar da cewa cikin wani farmaki da jami'an tsaron kasar suka kai yankin tsibirin Sinai cikin kwanaki 4 da suka gabata, sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda 16.

Tun a ranar 9 ga watan Favrayun da ya gabata ce, Sojoji da 'yan sanda suka kaddmar da yaki a kan 'yan ta'adda a tsibirin Sinai.

A ranar alhamis din da ta gabata, Kakakin rundunar sojin Masar Tamir Rafa'i ya ce daga lokacin da aka fara kai wanan farmaki, jami'an tsaro sun hallaka 'yan ta'adda 105, tare da rusa maboyarsu dubu daya da 907 a yankin tsibirin na Sinai.