Masar: Sojoji Sun Halaka 'Yan Tawaye 36 A Yankin Sinaa
Kakakin sojan kasar Masar Tamir al-Rufa'i ya fada a yau litinin cewa an kashe 'yan ta'addar ne a wani farmaki da aka kai musu a yankunan arewa da tsakiyar Sinaa.
Tamir Rufa'i ya ci gaba da cewa: A cikin kwanaki biyar da bayan nan, sojoji da 'yan sandan Masar sun yi nasarar gano makamai masu yawa da 'yan ta'addar suke amfani da su wajen kai hare-hare.
Bugu da kari, kakakin sojan na Masar ya sanar da kame wasu 'yan ta'addar su 345, haka nan lalata motar da aka makare da bama-bamai.
A ranar 9 ga watan Febrairu ne dai sojojin Masar tare da 'yan sanda su ka shelanta wani farmaki da suka bai wa suna: Sina 2018." da zummar kawar da 'yan ta'adda daga yankin.
Yankin Sina yana a matsayin wata tunga ce ta kungiyoyin 'yan ta'adda.