Nijar : Isufu Ya Taya Putin Na Rasha Murnar Sake Lashe Zabe
Shugaba Isufu Mahamadu na Jamhuriya Nijar, ya taya takwaransa na Rasha Vladimir Putin, murna sake zabensa a wani wa'adin shugabancin kasar ta Rasha.
Wata majiyar gwamnati ta shaidawa kamfanin dilancin labaren Xinhua cewa, Alhaji Isufu Mahamadu ya taya Putin murna sosai akan nasara da ya samu a zaben shuganacin kasar, wacce kuma ta nuna kyauna da goyan bayan da al'ummar Rashar ke masa akan ayyukan da ya sa gaba.
Isufu, ya jadadda wa takwaransa Putin cewa kasar Nijar na yaba wa ayyukan da Rasha ke gudanar wa a fanin kasa da kasa musamman a fannin samar da zaman lafiya, tsaro a fadin duniya, yana kuma mai fatan huldar dake tsakanin kasashen biyu zata daure don amfanar bangarorin biyu.
Kasashen Nijar da Rasha dai nada dadadiyar hulda tsakaninsu ta tsawan shekaru sama da arba'in, musamman ta fuskokin da suka shafi horo, tsaro da kuma ci gaba.