Masar : Al'Sisi Ya Musunta Kawar Da 'Yan Takaran Adawa
Shugaban kasar masar Abdel Fatah Al Sisi, ya yi fatali da zarge zargen cewa ya kawar da 'yan takara adawa da ake ganin zasuyi tasiri a zaben shugabancin kasar dake tafe.
Mista Al'sisi wanda ke bayyana hakan a wata hira da wani gidan talabijin din kasar, ya kuma yi kira ga jama'ar kasar dasu fito dafifi a zaben shugaban kasar da za'a gudanar a ranakun 26, 27 da 28 na watan Maris din nan da muke ciki.
Shugaba Al'sisi mai barin gado dake neman wa'adin shugabancin kasar a wa'adi na biyu zai fafata da dan takara guda, Musa Mostafa Musa wanda ke dasawa da shugaba Al'sisin.
'Yan takara da dama ne dai wadanda ake ganin cewa zasuyi tasiri a zaben na Masar aka kawar dasu daga tsayawa takara zaben ko kuma ake tsare dasu.
Daga cikin wadanda aka haramta wa shiga zaben da suka hada da Janar Sami Anan wanda aka dakatar jin kadan bayan sanar da anniyarsa ta tsayawa takara, sai kuma tsohon firayi ministan kasar Ahmed Chafiq wanda shi ma ake tsare da shi a wani Otel jin kadan bayan dawowarsa daga Hadadiyyar daular Larabawa saboda bayyana anniyarsa ta tsayawa takara zaben.