Masar: An Bude Taron Fasahar Musulunci Domin Fada Da Tsattsauran Ra'ayi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29312-masar_an_bude_taron_fasahar_musulunci_domin_fada_da_tsattsauran_ra'ayi
An bude taron ne na kasa da kasa a birnin Alexadaria na kasar Masar da zummar kalubalantar wuce gona da iri da sunan addini.
(last modified 2018-08-22T07:01:36+00:00 )
Mar 22, 2018 14:20 UTC
  • Masar: An Bude Taron Fasahar Musulunci Domin Fada Da Tsattsauran Ra'ayi

An bude taron ne na kasa da kasa a birnin Alexadaria na kasar Masar da zummar kalubalantar wuce gona da iri da sunan addini.

Hukumar al'adu da ilimi da ke karkashin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta shirya taron na kasa da kasa a jiya laraba, kuma zai ci gaba a yau alhamis.

Da akwai kwararru da masana ayyukan fasaha 50 da suka fito daga kasashen musulmi domin baje kolin kwarawarsu da kuma tattauna hanyoyin da za a bayyana kyawawan abubuwan da suke kunshe cikin addinin musulunci.

An bai wa taron taken Daga Chana zuwa Andulus, domin nuna ruhin fasaha ta musulunci.