Nijer:'Yan Boko Haran Sun Kashe Mutane 7 A Jahar Diffa
Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton' yan Boko Haram ne sun kai wani hari a kauyen Tumur dake jihar Diffa a cikin daren jiya wayewar wannan safiyar Juma’a inda suka kashe mutum bakwai tare da jikattaa wasu da dama na daban.
Rahotanni dake fitowa daga daga yankin Diffa na jamhuriya Nijar na cewa 'yan boko haram sun sake kai wani mumunan hari a garin Tumur a daren jiya wayewar safiyar wannan juma'a, inda suka kashe mutane kimanin bakwai.
Harin dai na yammacin jiya Juma'a a cewar rahotanni ya tilastawa sojojin kasar janyewa daga yankin sa'o'i kadan bayan da maharan suka farbawa garin.mazauna yankin sun shaida cewa 'yan boko haram din sun kuma kwashe kayayaki da dama kafin su bar wajen.
Wasu Rahotanni na daban sun ce mutum biyar ne aka kashe.
Yankin Diffa dake iyaka da Najeriya na fama da matsalar harin kungiyar Boko haram, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar jami'an tsaro da fararen hular kasar da dama da raba wasu na daban da mahalinsu, kamar yadda yankunan Tahoua da Tilabery ke fama da hare-haren 'yan tawaye da masu da'awar jihadi dake fitowa daga kasashen Mali da Burkina faso.
Kawo yanzu babu wani karin bayyani da ya fito daga bangaren hukumomin yankin da ma na kasar baki daya.