Sabon Rikicin Ya sake Kunno Kai A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29354-sabon_rikicin_ya_sake_kunno_kai_a_jamhuriyar_afirka_ta_tsakiya
Rahotanni daga jahuriyar Afirka ta tsakiya sun ce mutane da dama ne suka rasa rayukansu sakamakon artabun da aka yi tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a yankunan arewa maso yammacin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:31:36+00:00 )
Mar 24, 2018 11:51 UTC
  • Sabon Rikicin Ya sake Kunno Kai A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya

Rahotanni daga jahuriyar Afirka ta tsakiya sun ce mutane da dama ne suka rasa rayukansu sakamakon artabun da aka yi tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a yankunan arewa maso yammacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoto daga birnhin Bangui cewa, a cikin kwanaki uku da suka gabata an yi tashin hankali mai tsanani a yankunan arewa maso yammacin kasar, inda kungiyoyin 'yan bindiga suke ta kashe fararen hula.

Rahoton ya ce a cikin kwanaki uku da suka gabata, 'yan bindiga sun harbe wasu fararen hula dukkaninsu mata  a bainar jama'a.

Shugaban kasar Afirka ta tsakiya Faustin-Archange Touadéra ya bukaci majalisar dinkin duniya da ta sake shiri na musamman domin kai daukin gaggawa na tabbatar da tsaro a kasarsa.