Nijar : An Cafke Jagororin Kungiyar Fara Hula
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29374-nijar_an_cafke_jagororin_kungiyar_fara_hula
Rahotannin daga Jamhuriya Nijar na cewa 'yan sanda sun gudanar da samame na cafke jagororin kungiyoyin fara hula da suka shirya zanga zanga da mahukuntan birnin suka haramta.
(last modified 2018-08-22T11:31:36+00:00 )
Mar 25, 2018 17:47 UTC
  • Nijar : An Cafke Jagororin Kungiyar Fara Hula

Rahotannin daga Jamhuriya Nijar na cewa 'yan sanda sun gudanar da samame na cafke jagororin kungiyoyin fara hula da suka shirya zanga zanga da mahukuntan birnin suka haramta.

Mutanen da ake cafke sun hada da  Musa Changari na kungiyar fara hula ta AEC da Ali Idrissa na kungiyar CROSADE sai kuma Ussaini Maiga mamba na Jam'iyar MODEN Lumana FA.

Babu karin bayyani kan dalilin cafke mutanen, amma da yammacin yau Lahadi ne hadin kan kungiyoyin fara hula suka shirya gudanar da zanga-zanga da zaman dirshin duk da kashedin mahukuntan birnin. 

An dai zuba jami'an 'yan sanda masu yawa a birnin, a yayin da masu zanga zangar suka fara taruwa duk da haramcin da mahukuntan birnin suka yi.

Hukumomin Yamai dai sun ce matsalar tsaro da barazanar ta'addanci su ne sillan daukar matakin na haramta duk wata irin zanga zanga a daidai wannan lokaci musamman ma cikin tsakar dare.