Nijar : Mutum 10.625 Suka Kamu Da Cutar Tarin Fuka A Shekara 2017
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29396-nijar_mutum_10.625_suka_kamu_da_cutar_tarin_fuka_a_shekara_2017
Ma'aikatar kiwan lafiya a jamhuriya Nijar ta ce mutum dubu goma da dari shida da ashirin da biyar ne (10,625) ne aka gano cewa suna dauke da cutar tarin fuka ko tuberculosis) da turanci a shekara 2017 da ta gabata.
(last modified 2018-08-22T11:31:36+00:00 )
Mar 27, 2018 05:48 UTC
  • Nijar : Mutum 10.625 Suka Kamu Da Cutar Tarin Fuka A Shekara 2017

Ma'aikatar kiwan lafiya a jamhuriya Nijar ta ce mutum dubu goma da dari shida da ashirin da biyar ne (10,625) ne aka gano cewa suna dauke da cutar tarin fuka ko tuberculosis) da turanci a shekara 2017 da ta gabata.

Ministan lafiya na kasar ta Nijar ne Dakta Illiasu Idi Mai Nassara, ya bayyana hakan a yayin bikin ranar duniya ta yaki da cutar ta tarin fuka da ya gudana a ranar 24 ga watan Maris din nan.

Daga cikin mutanen da an gano cewa akwai 342 dake dauke da kwayoyin cutar HIV/VIH na AIDS ko SIDA.

Hakan dai a cewar ministan ya tabbatar da alakar dake tsakanin cututukan biyu wato babban tari da kuma SIDA.

A daya bangare ministan ya yaba sosai da ci gaban da aka samu kan yaki da cutar idan aka kwatanta sakamakon shekara 2012 zuwa na 2016 inda aka samu raguwar cutar ta hanyar jinya da kashi 81%.