Sharhi: Kammala Zaben Shugaban Kasa A Kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29454-sharhi_kammala_zaben_shugaban_kasa_a_kasar_masar
Tun a yammacin jiya ne aka fara kidaya kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar Masar, jim kadan bayan sanar da rufe dukkanin rumfunan zabe.
(last modified 2018-08-22T07:01:37+00:00 )
Mar 29, 2018 02:31 UTC
  • Sharhi: Kammala Zaben Shugaban Kasa A Kasar Masar

Tun a yammacin jiya ne aka fara kidaya kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar Masar, jim kadan bayan sanar da rufe dukkanin rumfunan zabe.

Hukumar zaben kasar Masar ta ce zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali, kuma tana sa ran za a kammala kidaya dukkanin kuri'un da aka kada daga nan zuwa ranar biyu ga watan Afirilu mai kamawa, kuma za a sanar da sakamakon karshe na zaben ne bayan kamala kidaya dukkanin kuri'un.

Wasu daga cikin mazabun sun sanar da sakamakon farko na adadin kuri'un da suka kirga, wanda ke nuni da cewa shugaban kasar ta Masar take kan karagar mulki Abdulfattah Sisi ne yake da mafi wan kuri'un.

Tun a 'yan watannin baya ne dai gwamnatin Abdulfattah Sisi ta fara daukar dukkanin matakai na murkushe duk wani dan siyasa da take ganinsa  amatsayin barazana, musamnman ma wadanda suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takara, inda gwamnatin ta Masar ta kame wasu ta garkame su a gidan kaso, wasu kuma aka firgita su tare da tilasta su janye takararsu.

Irin wannan mataki da gwamnati Sisi ta dauka, ya sanya babu wani dan takara da zai iya ja da shi, amma a maimakon yi gudanar da zaben tare da dan takara daya tilo wato shugaban kasa, an bar Musa Mustafa Musa wani dan siyasa a kasar, domin tsayawa takara wadda ba za ta iya yin wani tasiri ba a sakamakon zaben.

Kungiyoyin kare dimukradiyya na kasa da kasa sun yin tir da kakkausar murya  a kan irin wannan mataki na murkushe 'yan adawar siyasa da kuma yin mulki na bangare daya da shugaban kasar Masar da suka ce Al-sisi yana dauka, inda suke bayyana hakan da salon mulkin kama karya.

Duk da irin matakan da gwamnatin masar ta dauka na karfafa gwiwar jama'a domin su fito su kada kuri'a  a lokacin zaben, da hakan ya hada da bayar da kudade da abinci ga jama'a kyauta, da kuma yin amfani da dukkanin kafofin yada labarai na gwamnati wajen jan hankalin jama'a kan hakan, amma kusan kashi biyu bisa uku na wadanda suka cancanci kada kuri'a  a kasar ba su fito ba, wanda ko shakka hakan ba zai yi Al-sisi da masu mara masa baya dadi ba.

Abdulfattah Sisi wanda shi ne tsohon babban hafsan hafsoshin sojin kasar Masar a lokacin shugabancin Muhammad Mursi, ya yi amfani da matsayinsa wajen yi wa Mursi juyin mulki tare da jefa shi a gidan kaso.

A lokacin da ya karbi mulkin kasar ta Masar, Alsisi ya ce zai mika mulkin ga farar hula bayan dan kankanin lokaci, tare da daukar alkawalin cewa ba zai shiga siyasa ba, kuma ba zai tsaya takarar shugabancin kasar Masar a matsayin dan takara na siyasa ba, domin kuwa a cewarsa juyin mulkin da ya yi, ya yi hakan ne domin maslahar kasa, kuma maslaha ita ce ya shirya zabe ya mika wa farar hula mulki.

Da dama daga cikin masana siyasar kasa da kasa sun yi imanin cewa, saba alkawalin da Al-sisi ya yin a kin mika ragamar mulki ga farar hula, hakan ya saka shakku matuka a cikin zukatan mafi yawan al'ummar kasar masar a kansa da kuma manufofinsa, musamman abubuwan da ya yi bayan ya rikide ya koma shugaban farar hula, inda yake ci gaba da murkushe 'yan siyasa na kasar da karfin tuwo, baya ga haka kuma ya kasa kawo canjin da yake ikirari, tare da kasa kasa magance matsalolin tattalin arziki da kasar ta fada a ciki, da kuma kasa magance matsalolin rashin aikin yi a tsakanin matasa na kasar, duk da irin makudan kudaden da ya karba daga wasu sarakunan larabawa, har da wadanda ya mika wa wasu tsibiran kasar a kan makudan biliyoyin daloli.

Ba'a da bayan haka kuma, wani abu da mafi yawan al'ummar kasar Masar suka yi imani da shi, shi ne cewa, Al-sisi ya gaza wajen tabbatar da tsaro a kasar, duk da kasancewarsa tsohon babban hafsan hafsoshin soji na kasar ta Masar, wanda ya karbi mulki da bakin bindiga.