Masar : Al'Sisi Ya Lashe Zabe Da Gagarimin Rinjaye
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29466-masar_al'sisi_ya_lashe_zabe_da_gagarimin_rinjaye
Kafofin yada labarai na gwamnati a Masar, sun ce shugaba, Abdel Fattah Al-Sissi, ya lashe zaben shugaban kasar da aka kammala kada kuri'arsa a jiya Laraba da sama da kasha 90%.
(last modified 2018-08-22T07:01:37+00:00 )
Mar 29, 2018 11:52 UTC
  • Masar : Al'Sisi Ya Lashe Zabe Da Gagarimin Rinjaye

Kafofin yada labarai na gwamnati a Masar, sun ce shugaba, Abdel Fattah Al-Sissi, ya lashe zaben shugaban kasar da aka kammala kada kuri'arsa a jiya Laraba da sama da kasha 90%.

Bayanan sun kuma ce abokin hamayyarsa daya tilo, Musa Mostafa Musa, ya samu kashi 3% na yawan kuri'un da aka kada.

Dama kafin hakan da yammacin jiya, dan takaran Musa Mostafa, ya bayyana a cikin wata hira da wani gidan talabijin mai zaman kansa a Masar din cewa, ya amunce shan kaye a zaben, duba da kwarya kwarya sakamakon zaben da aka fara fitarwa.

Rahotanni daga kasar sun ce ba'a samu fitowar jama'a sosai ba a zaben da aka kwashe kwanaki uku ana kada kuri'arsa, duk da kiran da mahukuntan kasar suka yi da barazana cin tarar jama'ar da suka kaurace wa zaben.

Nasara Al'sisi a zaben bata zo da mamaki ba, kasancewar duk mutanen da ake ganin zasu yi tasiri a zaben an haramta masu tsayawa takara.