Shugaban Kasar Botswana Ya Yi Murabus
Shugaban kasar Botswana ya yi murabus tare da meka ragamar milkin kasar ga mataimakinsa
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa a wannan asabar shugaba Ian Khama na kasar Botswana ya sauka daga kan kujerarsa, watani 18 kafin wa'adinsa ya kare, sannan kuma ya meka jan ragamar milkin kasar ga mataimakinsa Mokgweetsi Masisi wanda kuma shi ne mutum na uku da ya riki babban matsayi da kuma yanzu zai jagoranci kasar da ya kasance ba daga cikin zuriyar Khama ba.
A yayin da yake gabatar da jawabin yin murabus din sa, Shugaba Ian Khama ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne domin amsar kirar da wasu 'yan siyasar kasar na rage wa'adin milkin kasar, sannan ya ce shi a karan kansa ba shi da sha'awar shiga siyasa domin ya nada wasu tsare-tsare masu mahimanci da zai iya taimakawa al'ummar kasar ko da kuwa ba ya kan shugabancin kasar.
Tun lokacin da kasar Botswana dake kudancin Afirka ta samu 'yanci daga kasar Birtaniya a shekarar 1966, zuriyar Khama ne ke milkin kasar.