Nov 22, 2018 08:00 UTC
  • Sabon Shugaban Kasar Brazil Jair Bolsonaro

Sabon Shugaban Kasar Brazil Jair Bolsonaro

Bayan da aka gudanar da bincike akan shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff da kuma tabbatar da laifi akanta dangane da cin hanci da rashawa, an dakatar da ita daga aiki na tsawon watanni shida. Hakan ya kawo karshen gwamnatin masu ra'ayin sauyi a karkashin jam'iyyar 'yan kwadago da ta fara daga 2003 tare Lula Da Silva.

Bayan da Rousseff ta sauka daga kan mulki, mataimakinta  Michel Temer ya maye gurbinta.

Sai dai duk da wannan sauyin da aka samu, dambaruwar siyasar kasar ba ta zo karshe ba. A cikin shekaru biyu na bayan nan kasar ta ci gaba da fuskantar matsalolin siyasa da tattalin arziki.

Michel Termer ya yi kokarin kawo sauye-sauye a cikin al'amurran tafiyar da kasar musamman a cikin tattalin arziki. Ya kuma jingina karuwar rashin aikin yi a cikin kasar da rashin sarrafa makudan kudaden tafiyar da gwamnati a karkashin shugabancin Roussef.

Sai dai duk da haka Temer bai sami karbuwa ba a tsakanin al'ummar kasar. Al'ummar kasar sun ganin cewa babu wani sauyi da su ka samu ta fuskar tattalin arziki a karkashin gwamnatinsa. Don haka titunan kasar su ka zama filin dagar gudanar da zanga-zanga da kuma taruka na nuna kin jinin gwamnati.

Dga cikin muhimman abubuwan da su ka faru a karkashin mulkin Temer shi ne zaben shugaban kasar da aka yi a wannan shekara ta 2018 wanda masu sharhi suke bayyanawa a matsayin wacce ta sauya alakar kasar ta Brazil

An yi zagane na farko na zaben a ranar 7 ga watan Oktoba na wannan shekara ta 2018. An yi shi ne tare da zaben 'yan majalisar dokoki da kuma na gwamnonin jahohin kasar.

Saboda tsohon shugaban kasar Lula Da Silva yana gidan kurkuku, ba zai iya tsayawa takara ba,an yi gogayya ne a tsakanin wanda ya gaje shi, wato Fernando Haddad da kuma Jair Bolsonaro wanda tsohon soja ne.

Bolsonaro ya sami kaso 46/3 a zagayen farko na zaben shugaban kasar. Shi kuwa Haddad ya sami kaso 29% na jumillar kuri'un da aka kada.

Bayan wannan zaben zagaye na farko ne wani mutum ya kai wa Bolsonaro hari da wuka. Ya kwanta a asibiti na wani lokaci. Bai kuma sami damar shiga cikin yakin neman zabe ba a wannan tsakanin kamar kuma yadda bai aminta ya yi mukabala ta gaba da gaba da Haddad ba, amma kuma ya kasance mai yawan tofa albrkacin bakinsa a cikin shafukan sadarwa na al'umma.

Saboda babu dan takarar da ya sami yawan kuri'un da ake bukatuwa da su, an sake yin wani zaben zagaye na biyu a ranar 28 ga watan Oktoba na 2018. Sakamakon karshe na zaben ya tabbatar da Bolsanaro a matsayin wanda ya lashe zabe da kaso 55%. Wanda yake bi masa kuwa wato Haddada yana da kaso 44/8.

Byan da aka sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben kasar, Bolsonaro ya bayyana cewa; Zai kre tsarin demokradiyya na kasar haka nan tsarin mulki. Ya kuma yi alkawalin cewa zai sauya makomar Brazil.

Har ila yau zababben shugaban kasar ya yi alakawalin rage aikata manyan laifuka da su ka zama ruwan dare a cikin kasar ta Brazil.

Damuwar da wani sashe na al'ummar kasar ta Brazil yake da shi dangane da zabar Jair Bolsonaro shi ne sha'awar da yake da ita na sake mayar da kasar akan turbar tsarin kama-karya na soja.

Akidarsa ta siyasa, irin ta kishin kasa mai zurfafawa ne da kuma amfani da hannun karfe.

Wannan ya jefa mutanen kasar cikin damuwa akan makomar 'yancinsu da hakkokinsu na tofa albrkancin baki.Duk da cewa masu kare shi suna bayyana ra'ayinsa da cewa irin wadanda aka saba da su ne a tsakanin masu ra'ayin mazan jiya.

 

                            ****

 

Nasarar da Bolsonaro ya samu, koma baya ne ga masu ra'ayin kawo sauyi ba a cikin Brazil kadai ba, a cikin fadin yakin Latin. A cikin shekarun bayan nan kasashe kamar su Argentina, Peru, Chile, da Columbia, sun hau turbar ra'ayin mazan jiya a siyasance,wato abinda yake faruwa yanzu a kasar Braliz.

Jami'iyyar masu ra'ayin kawo sauyi za ta zama ta adawa na tsawon shekaru hudu, wato zuwa wani wa'adin na manyan zabuka a kasar. Jam'iyyar ta yi mulki na tsawon shekaru 14 a kasar Brazil.

 

 

Taken da Bolsonari ya rika bayarwa a lokacin yakin neman zaben, haka nan kuma alkawullansa, sun sa an ba shi lakabin Trump na kasar Brazil.

Daya daga cikin abubuwan da Bolsonaro ya yi yakin neman zabe da su shi ne tabbatar da tsaro da zaman lafiya, saboda la'akari da yadda aikata laifuka ya watsu a kasar. Ya yi alkawalin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali akan titunan kasar ta Brazil. Hari la yau, ya yi alakawalin saukake hanyoyin mallakar makamai a tsakanin 'yan kasar.

Bugu da kari, zababben shugaban kasar ta Brazil ya nuna adawarsa zubar da ciki. Ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; Kudin Brazil aba za su tafi wurin kungiyoyin da ba na gwamnati ba, wadanda suke yada akidar zubar da ciki. Wannan zancen nashi ya jawo hankali magoya bayan akidar Roman Katolika ta addinin kirista.

 

A wurin mutanen Brazil da dama, sun zabi Jair Bolsonari ne domin rashin gamsuwarsu da siyasar tattalin arziki ta gwamnatin da ta shude ta masu ra'ayin sauyi.

 

A zangon farko na mulkin jam'iyyar masu ra'ayin sauyin, tattalin arzikin kasar ya bunkasa, sai dai daga baya ya fuskanci koma baya. Don haka mutanen kasar suke fatan cewa sabuwar gwamnatin da Bolsonaro zai kafa wacce ta yi Imani da budaddiyar kasuwa mai 'yanci daidai da sauran kasashen yankin da suke bin tsarin jari-hujja, suna fatan cewa zai kyautata tattalin arzikin kasar. Abin da yake da kamar wuya bisa la'akari da dabi'ar jari hujja.

 

 

Tags