Nijar : Ba Zamu Tattauna Da Boko Haram Ba_Isufu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29570-nijar_ba_zamu_tattauna_da_boko_haram_ba_isufu
Shugaba Isufu Mahamadu na Jamhuriya Nijar, ya bayyana cewa kasarsa ba zata tattauna da kungiyar boko haram ba.
(last modified 2018-08-22T11:31:38+00:00 )
Apr 02, 2018 10:57 UTC
  • Nijar : Ba Zamu Tattauna Da Boko Haram Ba_Isufu

Shugaba Isufu Mahamadu na Jamhuriya Nijar, ya bayyana cewa kasarsa ba zata tattauna da kungiyar boko haram ba.

Alhaji Isufu Mahamadu ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin din kasar, a jajibirin cikarsa shekaru 7 da mulkin kasar, inda kan cewa ko kasar zata iya tattaunawa da boko haram don ceto matan nan 39 na garin Ngalewa dake jihar Diffa da kungiyar boko haram ta sace, ya ce kasarsa ba zata tattauna da gungun 'yan ta'adda ba, kamar yadda hukumomin Najeriya suka yi.

Shugaban a cewarsa dakarun rundinar hadin gwiwa dake Nijar, tana ci gaba da samun galaba kan 'yan kungiyar Boko Haram, kuma bai fidda tsamanin cewa nan ba da jimawa ba za'a yi nasara kan kungiyar ta Boko Haram.