Masar:An Yanke Hukunci Kan 'Yan Uwa Musulmi 190
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29622-masar_an_yanke_hukunci_kan_'yan_uwa_musulmi_190
Wata Kotun hukunta manyan laifuka ta Sohag a Masar ta yanke hukincin dauri daga shekaru uku zuwa daurin rai da rai ga wasu mabiya kungiyar 'yan uwa musulmi 190 a wannan Laraba.
(last modified 2018-08-22T07:01:39+00:00 )
Apr 04, 2018 14:26 UTC
  • Masar:An Yanke Hukunci Kan 'Yan Uwa Musulmi 190

Wata Kotun hukunta manyan laifuka ta Sohag a Masar ta yanke hukincin dauri daga shekaru uku zuwa daurin rai da rai ga wasu mabiya kungiyar 'yan uwa musulmi 190 a wannan Laraba.

Kafar watsa labaran Alyaumu-sabi'i ta habarta cewa a wannan Laraba kotun hukunta manya laifuka Sohag ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wasu mabiya kungiyar 'yan uwa musulmi 35 bayan da ta kama su da laifin da hanu a alakar magarah. 

Har ila yau Kotun ta yanke hukuncin dauri daga shekaru uku zuwa 15 ga wasu 155 na daban, 61 daga cikinsu an yanke musu hukuncin daurin shekaru 15, wasu kuma 62 an yanke musu daurin shekaru 10 a gidan kaso, wasu 26 na daban kuma an yanke musu hukuncin dauri na shekaru biyar, sannan kuma sauran 6 an yanke musu hukuncin dauri shekaru uku, bugo da kari kotun ta bayyana cewa bayan wadannan mutane sun kamala zman gidan kaso, za su kasance karkashin sanya ido na jami'an 'yan sanda na tsahon shekaru biyu.

Su dai wadannan mutane an kama su ne a wani tsauni tare da tarin makamai masu yawa, inda kotun ta zarke su da ayyukan ta'addanci.