Masar : Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'ada 60 A Yankin Sina
-
wasu sojojin Masar a fagen daga
Rundinar Sojin kasar Masar ta sanar da kashe 'yan ta'ada 60 a wani samame da suka kai yankin Sina inda reshen 'yan ta'adan (IS) suka yi kaka-gida.
Kazalika Hadin gwiwar rundinar musamen ta sama da kuma dakarun na Masar sun raunana wasu 'yan ta'adan 40 da kuma lalata motocin su 27 a samamen na jiya Juma'a a kudancin birnin Rafah da kuma jihar Cheikh Zoueid dake arewacin Sina kamar yadda wani kakakin rundinar sojin kasar ya sanar a shafinsa na facebook.
Yankin na Sina dai ya jima yana fuskantar barazana 'yan ta'adan na reshen kungiyar (IS), kuma a mafi yawa sukan kai hare-haren ne kan 'yan sanda da sojoji tun bayan kifar da gwamnatin Muhammad Mursi a cikin shakara 2013.
ko a makon daya gabata kungiyar ta (IS) ta dauki alhakin kai wani hari a yankin na Sina da yayi sanadin mutuwar 'yan sanda 15.
kuma idan ana tune 'yan ta'adan yankin ne suka dauki alhakin kakkabo jirgin fasinja nan na Rasha a watan Oktoba bara a yankin na Sina da yayi sanadin mutuwar daukacin fasinjoji galibi 'yan yawan shakatawa na Rasha 224 dake cikin sa.