An Kai Hari Kan Dakarun MDD A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
Apr 10, 2018 18:57 UTC
Majiyoyin dakarun majalisar dinkin duniya masu gudanar da ayyukan wanzar da sulhu da zaman lafiya a jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun tabbatar da kai hari a kansu.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayar da rahoton cewa, wasu 'yan bindiga masu dauke makamai ne suka kaddamar da hare-hare a kusa da fadar shugaban kasar jamhuriyar Afirka ta tsakiya da ke birnin bangui a ranar lahadi da ta gabata, inda suka kashe mutane 2 da kuma jikkata wasu kusan sattin.
bayan faruwar lamarin dakarun majalisar dinkin duniya sun kame wasu daga cikin maharan, amma daga bisani kuma wasu daga cikin 'yan bindigar sun bude wuta kan dakarun na MDD, amma dai babu wanda ya rasa ransa daga cikinsu.
Tags