Ministan Harkokin Wajen Nijar Ya Yi Murabus
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar, Ibrahim Yakuba ya yi murabus daga mukaminsa, tare da janye jam'iyyarsa ta (MPN Kishin-kasa) daga kawancen jam'iyyu masu mulki na MRN.
Kafin hakan dai ministan ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, Firaministan kasar ya kira shi inda ya shaida masa cewa, shugaban kasar baya bukatarsa a cikin gwamnatinsa, wannan ne ya sa ya rubuta takardar murabus dinsa.
Tun ba yau ba dai ne ake ta yayata rashin jituwa tsakanin jam'iyyar ta (MPN Kishin-Kasa) da abokiyar dasawarta ta (PNDS Tarayya).
Saidai wanda ya fito fili shi ne sanarwar da jam'iyyar ta MPN ta fitar a kwanan baya na nuna rashin gamsuwa da sabon kundin tsarin zabe na kasar wanda ta ce sam bai tanadi yadda za'a yi sahihin zabe ba a shekara 2021.
Haka ita ma ministar yada labarai ta kasar Hadizatu Kubra Abdullahi ta jam'iyyar MPN Kishin- Kasa din ta ajiye mukaminta.
Tuni dai gwamnatin kasar ta maye gurbin Ibrahim Yakuba da Kalla Hankurau wanda ke zaman mamba a kwamitin koli na jam'iyyar PNDS Tarayyar mai mulki, da aka taba zarga da bayar da kwangila ba bisa ka'ida ba, lokacin da yake ministan gine-gine.