An Sace Wani Dan Kasar Jamus A Nijar
Apr 12, 2018 11:15 UTC
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce an sace wani Bajamushe da ke gudanar da ayukan jin-kai a kusa da iyakar Mali.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Alhamis, gwamnatin ta Nijar ta sanar da cewa wasu 'yan bindiga kan babura sun sace wani jami'in agaji dan kasar Jamus mai suna Joerg Lange a garin Inates na jahar Tilabery dake iyaka da kasar Mali.
An sace jami'in ne a yayin da yake komawa daga ayukan agaji a arewacin yanki, shi dai wannan yanki ya fuskanci hare-haren ta'addanci kan jami'an tsaro da fararen hula daga kungiyoyi masu da'awar jihadi da ke da alaka da al-Qaeda da Kungiyar IS.
Kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani a kan 'yan bindigar.
Tags